Garaɓasar

GIDAUNIYAR OPEN ARTS

GARAƁASAR BUGA LITTATTAFAI KYAUTA!

Gidauniyar Open Arts, Kaduna ta samar da dama ga mata marubuta daga Arewacin Nijeriya domin su aiko da littattafan labaran da suka rubuta ko suke kan rubutawa a cikin harshen Ingilishi da Hausa don shiga cikin samun garaɓasar buga littattafai kyauta.

Bayani Game Da Garaɓasar:

Wannan garaɓasa ta marubuta mata ce kurum daga Arewacin Nijeriya da suke rubutu cikin harshen Ingilishi da Hausa. Idan an zaɓi littattafan da aka aiko da su za a biya marubutan kuɗin rubuta littattafan da aka zaɓa. Haka kuma marubutan za su samu horo na musamman daga masana don inganta ayyukansu na rubutu. Za a kuma buga littattafan da suka fi burgewa kyauta a cikin harshen Ingilishi da Hausa.

Abubuwan Da Marubutan Za Su Amfana Da Su:

  1. Horo na musamman:

Za a ba matan da aka zaɓi littattafansu horo na musamman domin inganta ayyukansu na rubutu da sanin salailan rubutu na zamani.

2. Aji na Musamman:

Za a kuma shigar da matan cikin aji na musamman don koya musu dabarun rubutu da yadda ake tsara da tace labarai da kuma yadda ake samar da rantsattsen littafi irin na zamani.

3. Haɗuwa da Gwanaye:

Matan da aka zaɓi littattafan nasu za su samu damar haɗuwa da gwanaye a fagen rubutu domin sanin makama da yadda za su zama abin nuni a fagen rubutu nan gaba. 

4. Haɗuwa-ta-ka da ‘Yan uwa Marubuta:

Za a samar da dama ga marubutan da aka zaɓi littattafansu su tattauna da juna domin ƙaruwar kansu, haka kuma za su haɗu da ƙwararru a fagen rubutu domin inganta rubutun da marubuta.

5. Za a Shirya Tarurruka na Musamman na Sauraren Karatu:

A wajen waɗannan tarurruka ana fatar marubutan su samu horo na musamman da kuma karanta wa duniya irin rubuce-rubucen da suke a kai, don a tallata fasaharsu.

6. Za a Taimaka wa Marubutan ta Fuskar Fassara Ayyukansu:

Wasu daga cikin littattafan da aka zaɓa za a ƙoƙarta fassara su domin su samu isa ga sauran al’ummar duniya.

7. Buga Littattafan:

Daga ƙarshe dukkan littattafan da aka zaɓa za a buga su cikin Hausa da Ingilishi domin ƙaruwar al’umma, a duk faɗin duniya.

ƘA’IDOJIN SAMUN WANNAN GARAƁASA

Dama ce ga mata marubuta kurum daga Arewacin Nijeriya da suke da rubutaccen littafin labari na Ingilishi ko Hausa a hannu ko za su iya kammala rubutawa su turo kafin ranar da aka ajiye domin rufe shiga samun garaɓasar.

A turo da cikakken littafin tare da ɗan taƙaitaccen tarihin marubuciya zuwa ga wannan adireshin imel: 

biba@openartsworld.org 

RANAR DA ZA A RUFE KARƁAR SAƘON LITTATTAFAI

31 Ga Watan Mayu 2024

Garaɓasar Ta Wanzu Ne Da Haɗin Gwiwar: Ford Foundation.