Raina Kama!

‘Bana Jin yadda ake yayata bukin HIFAB 2022 zai yi armashi da gaske’ wannan shi ne abin da yake min yawo a can wani loko na zuciyata, sakamakon takaddama da ake tsakanin zuciyoyina akan taron da za a gudanar na bana. Ni kaina Ina da shakku ko kokwanto akan yiwar abin saboda halin yau da Kuma yadda muke ji a kafofin yada labarai cewa Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohi dake a rukunin masu fama da tashin tashina, sannan ga wahalar man fetur a kasa da Kuma uwa uba rashin Naira a hannun Ya ayyuhan nasu.

Amma duk da haka akwai zuciyar da ta bani kwarin gwiwa na cewa in je kawai in tayi ruwa rijiya in ta kiya kuma Masai.
Shi yasa na shirya na tafi, da nufin in taron bai yiwu ba in wuce Kasuwar Barci (ko har yanzu haka sunanta yake?) Oho!
Na dunfaro ginin gidan Arewa, Ina sake sake , kamar Biki, kamar Wani taro, Kai Ina Jin watakila Yan baje kolin Kasuwar Duniya ne suka zo Arewa House. A haka na isa babbar Kofar shiga harabar gidan.
Jami’an tsaron da aka tanadar ne su ka mini iso har in da ake tarban baƙi.
Yanzu ne na Kara tabbatar da cewa lallai wannan wuri da fasalin tsarinsa na Taron HIFAB ne, Haba! Nan take na fito da lasisi da aka bani yayin shigowa na makala tare da yin gyaran murya. Babban jigo ya iso.
Kasancewata a gurbin farko ya sanya aka mini tarbo da abin bikin a cikin jaka ciki har da abin da na dangana da abokin ɗebe kewa.
Na zauna da kyau Ina kulla Zare da Abawa, wai nine a Babban dakin taro Wanda ya Yi min kama da irin Wanda ake sabga ko walimar Ango da Amarya. Yanzunma wa ya sani ko harda ɗaurin auren Marubuta a wurin.

Bayan zama na iyayen taro suka hallaro ciki har da kakar amarya da aka kudurta nuna ma duniya mahimmancinta a ranar, ga babban baƙo uban ƙasa har ma da delegates bila adadi.

Abin da ya fara tsaya min a rai shine yadda na ga ƙarfi da yaji manyan baƙi na shirin maida ƴar uban Amarya mowa a taron bikin, amma kakan amarya ba ta bari haƙansu ya cimma ruwa ba ta nuna lallai Amaryar ba ƴar gaban goshi kaɗai ce ba, ita ce bugun ƙalbin su da ta kasance abar Alfahirinsu.
Shin na ambaci cewa bikin yini muka yi aka kwana aka kuma yini, an ci an sha an gwangwaje, a lokacin da na ke ganin bari na ware sai Alhaji Musa Ɗan ƙwairo ya bayyana, mutumin da na taso ina jin wakokinsa a radiyon mahaifina, nan ya baje fikirarsa ban kammala tsimuwa ba sai ga Malam Mamman shata, nan ta ke na yi suman daɗi don ko a mafarkin ido biyu ban taɓa hango hakan a kusa ba, bayansu ga sha’irai haziƙai kana aka rattabo mana tarihin iyaye da kakannin amarya.
Mun ci abinci har ma da kaza, tsire, gurasa da awara, har ma da ababen jiƙa maƙoshi
Taron bikin HIBAF 2022 ya kasance ɗaya tamkar dubu, ya bayyana asali, al’adu har ma da Fasahohin amarya Hausa.